Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Mutum 8 Suka Mutu a Najeriya Ranar Litinin


Hukumar sa ido kan cututtuka masu yaduwa (NCDC) a Najeriya ta tabbatar da cewa an samu karin mutum 288 da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar abinda ya sa gaba dayan adadin ya kai 44,129.

Hukumar ta NCDC ta bayyana hakan ne a shafin ta na Twitter a daren ranar Litinin 3 ga watan Agusta, ta kuma ce an samu mutum 8 da suka mutu sakamakon cutar.

Ya zuwa yanzu, mutum 20,663 suka warke daga cutar aka kuma sallame su daga asibiti mutum 896 kuma suka mutu a jihohi 36 ciki har da birnin Tarayya Abuja.

Hukumar ta ce an samu sabbin alkaluman ne daga jihohi 15 da suka hada da: Lagos (88), Kwara (33), Osun (27), birnin tarayya Abuja (25), Enugu (25), Abia (20), Kaduna (17), Plateau (13), Rivers (13), Delta (10), Gombe (8), Ogun (4), Oyo (3), Katsina (1), sai kuma Bauchi (1).

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG