Adadin wadanda suka mutu a Amurka sanadiyyar cutar coronavirus ya zarce dubu dari, a cewar alkaluman da kasar ta fidda ranar Laraba 27 ga watan Mayu.
Wannan adadin ya wuce adadin mace-mace da aka samu a kowace kasa sanadiyyar wannan annobar, nesa ma ba kusa ba, inda ya yi matukar dara na kasar Burtaniya, wadda ke da adadin 37,000 wanda shi ne na biyu a yawa a duniya, a cewar Jami'ar Johns Hopkins.
Hakazalika, daga cikin adadin masu fama da cutar miliyan 5.6 a duniya, miliyan 1.6 a Amurka su ke.
Shugaban kasar Donald Trump dai na kare kansa daga masu sukarsa wadanda ke alakanta yawan masu kamuwa da cutar da kuma masu mutuwa kan abinda suka kira rashin mayar da hankali kan cutar yadda ya kamata da Shugaban kasar ya yi.
Trump ya ce, da bai dau irin matakin da ya dauka ba, da adadin ya fi haka.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 23, 2021
Jirgin Hukumar Sama Jannatin Amurka Ya Isa Tashar Sararin Sama
-
Fabrairu 22, 2021
COVID-19 :Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Kusa Rabin Miliyan A Amurka
-
Fabrairu 20, 2021
Amurka Ta sake Komawa Cikin Yarjejeniyar Sauyin Yanayi A Hukumance
-
Fabrairu 17, 2021
Texas-Dussar Kankara Ta Haifar Da Dauke Wuta A Gabashin Amurka
Facebook Forum