Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Trump Ya Nace Kan Amfani Da Chloroquine


Muhawara kan alfanun amfanin da maganin cutar Malaria wajen jinyar Amurkwan da su ka kamu da cutar Coronavirus na janyo takaddama tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da babban masanin cututtuka masu yaduwa na kasar, Dakta Anthony Fauci.

Yayin da kulluyaumin ake ganin karin darurruwa a yawan mutanen da ke mutuwa a Amurka sanadiyyar Coronavirus, Trump ya kan nuna cewa amfani da maganin Hydroxychloroquine na iya zama fa'ida, inda ya kan kira maganin, "mai iya canza lamari" wajen ceto rai.

“Me za a rasa? A sha kawai,” abin da shugaban ya fada kenan a taron manema labarai a fadar White House a karshen makon da ya gabata.

Ya ci gaba da cewa “lallai ina ganin ya kamata a sha, amma kuma zabi ya rage gare su, da kuma likitoci."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG