Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19:  Za A Raya Sunan Mai Kwarmato, Dr. Li Wenliang, a Amurka


Dr Li Wenliang kafin rasuwarsa

‘Yan Majalisun Tarayyar Amurka na dada goyon bayan wani kuduri na canza sunan hanyar da ta gitta gaban Ofishin Jakadancin China da ke birnin Washington na nan Amurka zuwa sunan Dakta Li Wenliang, dan kwarmaton nan da cutar COVID-19 ta kashe wanda China ta danne yinkurinsa na yin gargadi ga duniya game da illar cutar corona.

“Ina mai alfaharin gabatar da kudurin doka na canza sunan hanyar nan da ta bi gaban Ofishin Jakadancin China zuwa sunan Dakta Li,” a cewar ‘yar Majalisar tarayyar Amurka Liz Cheney mai wakiltar Wyoming yayin da ta ke gabatar da kudurin dokar a Majalisar Wakilai ranar Alhamis.

Ta kara da cewa, “Allah sa wannan ya zama wata tunatarwa ta dindindin ga duniya da kuma gwamnatin China cewa daga karshe dai dole sai gaskiya ta bayyana, da cewa kuma ba za mu taba mancewa da jajircewar Dakta Li ba da kuma cewa dole a tuhumi Jam’iyyar ‘Yan Kwaminist mai mulkin China saboda illar da karyarsu ta yi ga duniya.”

Facebook Forum

Arewa A Yau

Arewa A Yau
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:47 0:00
XS
SM
MD
LG