Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cuba Na Nazarin Hana Mutane Zirga-zirga


Shugaban Cuba Miguel Díaz-Canel

Jami’an kasar Cuba sun ce ana shirin sanya sabon matakin hana zirga zirgar jama’a da ababen hawa a matsayin wani bangare na kokarin rage yaduwar cutar coronavirus a Havana babban birnin kasar. 

Gwamnan Havana Reinaldo Garcia Zapata ya fada a jiya Alhamis cewa dokar hana fita daga karfe 7 na yamma zuwa 5 na safe za ta fara aiki daga ranar Talata mai zuwa.

Zapata ya kuma sanar da hana zirga zirga daga babban birnin na Cuba zuwa wasu lardunan. Ya ce gwamnati za ta sake duba tasirin sabbin matakan bayan kwanaki 15.

Kasar Cuba dai ta iya shawo kan yaduwar annobar COVID-19 kusan gaba daya ta hanyar killace wadanda suka kamu da cutar da kuma gano wadanda suka yi cudanya da su.

Facebook Forum

Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG