Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Cizon Sauro Ta Hallaka Mutane da Dama A Sokoto


Gwamnan Sokoto Waziri Aminu Tambuwal

Matsanancin cutar dai ta fi kamari a wasu unguwannin Sokoto kamar Tudunwada da Marina da kuma unguwar Sarkin Adar Gwandu

A unguwar Sarkin Adar Gwandu dake cikin birnin Sokoto mutane kimanin dari ukku ne suka kwanta a karamin asibitin dake wurin.

Mazauna unguwar sun bayyana rashin rayuka da dama a unguwar sanadiyar cutar wadda suka dauka tamkar wata annoba. Wata tace rayukan da aka rasa cikin unguwar sun kai hamsin saboda cutar.

Malam Habib Usman yace yanayin zazzabin nada ban tsoro matuka. Da zara mutum ya kamu da cutar koina a jikinsa sai ya dauki ciwo.Wasu kafin a kaisu asibiti rai yayi halinsa.

A lissafin gwamnati mutane biyar ne suka rasa rayukansu sanadiyar cutar amma gwamnatin tace tana daukan matakan gaggawa domin shawo kan cutar.

Dr Balarabe Shehu Kakale kwamishanan kiwon lafiya na jihar yace da jin labarin barkewar cutar suka dauki matakai shida na taimakawa wadanda suka kamu da cutar

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG