Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Ebola Na Kara Yaduwa


Jinyar cutar Ebola.

A wani al'amari mai karkada hanji, mugunyar cutar nan ta Ebola ta kama wani ma'aikacin Majalisar Dinkin Duniya a Kongo. Rahotanni na nuna cewa cutar na dada yaduwa.

Wani ma'aikacin Majalisar Dinkin Duniya a gabashin Janhuriyar Dimokaradiyyar Kongo ya kamu da cutar Ebola, wanda shi ne na farko tun bayan da cutar ta sake bulla a wannan karon, a cewar shugabar tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da zaman lafiya a Kongo.

"Ina mai bakin cikin shaida maku yau cewa mun samu labarin cewa wani abokin aikinmu da ke Beni ya kamu da cutar Ebola kuma yanzu haka ana kan yi masa jinya," a cewar Laila Zerrougui a wata wasikar da ta rubuta, wadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya samu.

Labarin na zuwa ne a daidai lokacin da jami'an kiwon lafiya ke gargadin cewa yawan yaduwar cutar ta Ebola ya ribanyu har ma da dori tun daga watan Satumba.

Facebook Forum

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Aminu Saira

Aminu Saira
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00
Karin bayani akan Nishadi
XS
SM
MD
LG