Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Korona: Yadda Na Makale a Abuja – Obiezu


Tedros Adhanom Ghebreyesus

A wata kasidar da dan jarida Timothy Obiezu ya rubuta game da kalubalen jinya a mawuyatan lokuta irin na annobar cutar korona, ya ce hatta asibitin da ya kamata mahaifinsa ya rika zuwa ganin likita saboda cutar kansar da ya ke fama da ita, ya zama daya daga cikin fagagen dagar da Najeriya ke fafatawa da cutar korona.

“Wannan doka ta killace mutane ta na shafa ta kamar yadda ta ke shafar sauran miliyoyin mutane a fadin Najeriya. Hukumoni sun dau wannan matakin ‘yan makonni bayan samun matum na farko dauke da cutar korona a ranar 27 ga watan Fabrairu. Yanzsu na makale a gidana amma ina kokarin ganin ba na zaman banza.” A cewar Obiezu.

Ya ce bayan makwanni biyu kawai da tarewa sabon gidansa da ke gundumar Wuye na Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja hukumomi su ka yi shelar daukar matakan killace mutane a karshen watan Maris.

Coronavirus Africa
Coronavirus Africa

Dokar hana fitar ta sa akasarin mutane na zama cikin gidajensu, saboda haka har yanzu ban san galibin makwabta na ba. To amma kariya ta mai suna Sophie ta na dauke ma ni kewa.

Dokar killacewar ba ta hana dan yawatawa da kare ba, don haka na kan dan yi yawo da ita saboda ta san sabon wurin. Wani sa’in ma na kan dan yi gudu da ita saboda yi motsa jiki kuma in ji garau.

Obiezu ya ce bayan da mahaifinsa mai shekaru 72 ya samu sauki daga cutar kansa, sai aka ce su rika kai shi wurin likita loto-loto. Su ka ga ai wannan ba matsala ba ce. Sai bayan da aka bayyana samun mutum na farko da cutar korona mako daya bayan nan. Kuma Asibitin koyarwa na Jami’ar Jahar Lagos na daya daga cikin asibitocin da aka yi gwaje gwajen.

Cikin ‘yan makwannin da su ka biyo baya, harkokin yau da kullum sun yi ta fuskantar karuwar barazana saboda karuwar cutar, har sai da aka dau wannan mataki. Lagos ne inda cutar ta korona ta fi tsanani a Najeriya.

Yanzu dokar killacewar ta kai makwanni biyar ta na aiki. A farkon wannan satin, Shugaban Najeriya ya bayyana cewa ranar Litini 4 ga watan Mayu za a sassauta dokar hana fitar saboda a rage radadinta.

To amma ganin yadda adadin masu dauke da cutar ta korona su ka kai fiye da 1,900 - akasari a Lagos da Abuja - Najeriya za ta fuskanci yaduwar cutar sosai tsakanin jama’a. Kuma ganin yadda miliyoyin mutane ke ta gararanba kan tituna, Allah kawai ya san abin da hakan zai haifar.

Facebook Forum

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG