Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Kwalara Ta Barke a Sudan Ta Kudu


Yaro da ya kamu da cutar kwalara a Sudan ta Kudu
Yaro da ya kamu da cutar kwalara a Sudan ta Kudu

An samu barkewar cutar kwalara a kasar Sudan Ta Kudu saboda gurbatacen yanayi da cukoson jama'a a wuri daya.

Sudan ta Kudu na fama da annobar yaduwar cutar kwalara inda tayi sanadiyar rasa rayukan mutane 18. Akalla an san mutane 170 dauke da cutar a ‘yan kwanakin nan.

Ministan lafiya na Sudan ta Kudu Riek Gai Kok ya fadawa manema labarai cewa annobar ta fara ne daga cinkoson a sansanin ‘yan gudun hijira da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa a babban birnin kasar, Juba, inda dubban mutane ke fakewa a sanadiyar yakin basasa.

Kwalara cuta mai shiga jikin mutum cikin gaggawa tana kuma haddasa gudawa, da ‘kafe ruwan jikin mutum idan har ba’a bata kulawa mai kyau ba. Ana samunta ne ta shan ruwan da ba’a tace ba da cin abinci maras tsabta. Wannan wata matsala ce da ake samu a sansanonin ‘yan gudun hijira, inda da yawa ke amfani da guri ‘daya.

XS
SM
MD
LG