Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Kwalara Ta Barke A Yankin Darfur Na Kasar Sudan


Wadansu yara suna jira iyayensu a dakin shan magani

Hukumar kiwon lafiya ta duniya tace tana kokarin shawo kan mummunar cutar shawara data barke a yankin Darfur na kasar Sudan.

Hukumar ta kiwon lafiya ta fada jiya talata cewa, tana hada kai da gwamnatin Sudan wajen samun alluran riga kafin cutar har kusan miliyan biyu da rabi domin mazauna yankin. Hukumar tace wata hadakar kasa- da kasa kan alluran rigakafi ce zata samar da alluran, wannan hadakar gamayyar kamfanonin harhada magunguna ne, wadanda suke aiki tare da Majalisar Dinkin Duniya.

Hukumar ta bada labarin cewa cutar ta barke ne a karshen watan Satumba, tun lokacin ta sami rahoton mutane 358 sun kamu da cutar, wasu 107 kuma sun riga mu gidan gaskiya. Wadnada suke zaune a tsakiyar yankin na Darfur, sune cutar tafi yiwa barna.
Da yake magana da Muriyar Amurka ta woyar tarho daga Khartoum, wakilin hukumar kiwon lafiya ta duniya a Sudan Anshu Banerjee, ya bayyana cewa za a fara aikin riga kafin cikin makonni uku masu zuwa, kuma za a yi mako biyu ana gudanar da shi.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG