Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Kwalara ta Kashe Mutane 7 a Jihar Kano


Wata mai fama da kwalara
Wata mai fama da kwalara

Mutane kimanin bakwai sun mutu daga cutar kwalara a yankin Badawa - Galedina a karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano, bisaga bayanin wani shugaban kiwon lafiyar jihar.

Mutane kimanin bakwai sun mutu daga cutar kwalara a yankin Badawa - Galedina a karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano, bisaga bayanin wani shugaban kiwon lafiyar jihar.

Shugaban sashin lafiya na karamar hukumar, Alhaji Mu’azu Doka, ya fadiwa hukumar labarai ta Nigeriya a Kano cewa marasa lafiya 68 ne ke karbar magani.

Doka yace 29 cikinsu suna asibitin cututtuka (IDH) a kano, da kuma sauran 39 suna sauran asibitoci.

“Wannan barkewa, dun da ta fara kwanakin baya da suka wuce, zuwa yanzu ta dauke rayuka bakwai.”

“Mun bawa fiye da mutane 71 magani, musammam wadanda basu da manyan cututtuka,” yace.

Doka yace karamar hukumar Sayi ta rarraba magunguna kimanin N650,000 domin maganin marasa lafiya. Bisagareshi, yace, shugabannin lafiya na wannan yankin sun ziyarci mutanen da suka kamu da niyyar basu taimako nagari.

Ya kuma ce, sashin lafiya sun baiyyana kwashe ruwan yankin daya kamu.
Doka ya danganta sabbin cututtuka da yanayi mai kazanta, yanda ya karfafa bukatar yin tsabta hadi da tsabtace yankin da suke.

Yace, “Akwai kazanta sosai a yankin, don haka dole mutanen wurin su tashi kan kalubalen tsabtace kewayen yankin su.”

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG