Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Polio Ta Bulla a Kasar Syria


Ma'aikaciyar lafiya tana ba jaririya maganin rigakafin Polio a kasar Syria

Hukumar Kiwon lafiya ta Duniya ta tabbatar da kamuwar yara 10 a lardin Deir al-Zour na yankin arewa maso gabashin Syria.

A bayan mummunar ukubar da al'ummar kasar Syria suke fama da ita a sanadin yakin basasa, hukumomin kiwon lafiya na duniya sun ce an samu bullar cutar shan inna ko Polio a kasar, kuma tana iya yadiuwa har zuwa wasu kasashen ma in ba a yi hattara ba.

Cutar Polio, tana iya haddasa nakasa ko kuma mutuwa a wasu lokutan, kuma ta fi kama yara 'yan kasa da shekara 5.

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya (WHO), ta tabbatar da cewa an samu kwayoyin cutar Polio a samfurin da aka auna na yarab 10 a lardin deir al-Zour dake arewa maso gabashin kasar.

Akasarin wadanda suka kamu da cutar ta Polio a kasar Syria, yara ne 'yan kasa da shekara 2, watau an haife su ne kuma suka kamu da cutar duk a lokacin da ake yaki a wannan kasa.

An kiyasta cewa kafin barkewar yaki, kashi 91 cikin 100 na yaran kasar Syria su na samun rigakafin cutar Polio a 2010, amma a tsakiyar yakin ya zuwa shekarar 2012, kashi 68 cikion 100 na yaran kasar kawai suke iya samun wannan rigakafi.

Barkewar cutar Polio a kasar Syria, alama ce ta irin abubuwan da suke wakana idan tsare-tsaren kiwon lafiyar jama'a na kasa suka durkusa. babban abin damuwa a yanzu shi ne akwai yara kimanin rabin miliyan a kasar ta Syria wadanda ba a samu sukunin ba su maganin rigakafin cutar Polio ba.

Hukumar WHO ta yi gargadin cewa akwai hatsari sosai na yaduwar wannan cuta zuwa kasashe makwabta inda 'yan gudun hijirar Syria ke kwarara. Yanzu haka dai an kaddamar da gagarumin yunkurin yin rigakafi ma yara a kasashen Lebanon, Jordan, Iraq, Turkiyya da Masar.

A wasu sassan duniya kamar Najeriya da Pakistan da Afghanistan, an samu gagarumin ci gaba a yaki da cutar ta Polio. An samu raguwar kashi 40 cikin 100 na yawan kamuwa da cutar Polio a wadannan kasashen. A yankin kudancin Afghanistan ma, yau shekara guda ke nan ba a samu yaro ko guda daya da wannan cuta ba.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG