Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar shan inna ta gurgunta yara hudu a jihar Zamfara


Wata tana ba yara maganin cutar shan inna
Wata tana ba yara maganin cutar shan inna

Cutar shan inna ta gurgunta yara hudu daga kananan hukumomi uku na jihar Zamfara cikin watanni shidda da suka shige.

Cutar shan inna ta gurgunta yara hudu daga kananan hukumomi uku na jihar Zamfara cikin watanni shidda da suka shige.

Babban darektan kiwon lafiya matakin farko a Najeriya Dr. Ado Mohammed ne ya bayyana haka a Gusau shelkwatar jihar, yayin kaddamar da kamfen yaki da cutar shan inna, wanda ya sami halartar shugabannin addini da sarakunan gargajiya daga jihohi goma sha tara na arewacin kasar.

Dr. Mohammed ya bayyana cewa, kananan yara hudu da suka gurgunta sakamakon kamuwa da cutar tsakanin watan Janairu zuwa yanzu, sun fito daga kananan hukumomin Bukkyum da Maru da kuma Zurma.

Bisa ga cewarshi, an sami biyu a Maru yayinda aka sami daya a karamar hukumar Bukkyum daya kuma a Maru. Darektan lafiyan ya bayyana damuwa ganin yadda kananan yara suke ci gaba da rasa rayukansu da kuma nakasa ta dalilin kamuwa da cutar shan inna duk da yake ana iya shawo kanta.

Ya kuma bayyana takaicin katse hanzarin kananan yara da cutar ke yi sakamakon rashin maida hankali wajen gangami da bada hadin kai tare a daukar kwararan matakan shawo kan cutar.

A cikin jawabinsa, Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya jadada bukatar ganin sarakunan gargajiya da shugabannin addinai sun hada hannu wajen wayar da kan jama’a dangane da illar cutar shan inna. Ya kuma yi kira garesu, su bada gagarumin goyon baya domin ganin an cimma burin shawo kan cutar a kasar kafin karshen shekara ta dubu biyu da goma sha uku kamar yadda aka kiyasta.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG