Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alama Shugaban Amurka Zai Yi Watsi Da Yarjejeniyar Nukiliya Da Iran


Shugaban Amurka Donald Trump da Yariman Saudiya Muhammad Bin Salman
Shugaban Amurka Donald Trump da Yariman Saudiya Muhammad Bin Salman

Yayinda yake karban bakuncin Yariman Saudiya Muhammad Bin Salaman shugaba Donald Trump ya ce a shirye yake ya yi watsi da yarjejeniyar da aka cimma akan nukiliyar Iran har da fadawa Yariman ya sa ido ya ga abun da zai faru

Shugaban Amurka Donald Trump bisa dukkan alamu a shirye ya ke ya yi watsi da shawarwarin da manyan hafoshin mayakan Amurka suke bashi, yayinda gwamnatinsa take ci gaba da tunanin hanyar da ta fi dacewa ta tunkarar Iran.

Trump yana fuskantar wa'adin ya sake sabunta yarjejeniyar da Amurka da wasu kasashen duniya suka kulla da Iran. Jiya Talata shugaban ya nuna cewa bashi da fargabar ya janye Amurka daga yarjejeniyar, idan sauran kasashe da aka kulla yarjejeniyar da su basu amince a gudanar da sauye sauye kan yarjejeniyar ba.

"Abububawa marasa kyau suna faruwa a Iran, shugaban na Amurka ya fada, yayin da yake karbar bakuncin Yerima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman, wanda ya kai masa ziyara a fadar White House jiya Talata.

"Batun sabunta yarjejeniyar zai taso wata mai zuwa, zaka ga abunda zai faru," shugaban na Amurka ya fada.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG