Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alamu Demba Ba Baya Cikin ‘Yan Wasan Da Zasu Wakilci Kasar Senegal.


Demba Ba, a wasan cin kofin nahiyar Afirka na shekara ta 2012.
Demba Ba, a wasan cin kofin nahiyar Afirka na shekara ta 2012.

Za’a dai a fara wasan cin kofin nahiyar Afirka a kasar Guinea, takwas ga watan Janairu na shekara mai zuwa ta 2015, amma har yanzu dai ba wani labarin ko Koch Alain Giresse na kungiyar kasar Senegal zai kira Demba Ba, domin buga wasanni masu zuwa.

Demba Ba, tsohon dan wasane wanda ya buga wasa da shahararrun kulob na duniya kamar West Ham, Newcastle United da Chelsea, yakuma zura kwallaye har goma sha shida a raga a bayyanar wasanni goma sha tara.

Koch Alain Giresse, dai baiyi amfani da Demba Ba a wasan da sukayi na karshe don shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka, dalilin Koch din na yin hakan shine yace, ‘dan wasan ya yaji ciwo a hannu, amma shi ‘dan wasan Demba Ba, yafito fili ya karyata wannan dalili.

Kasar Senegal din dai tayi kunnen doki a rukunin da take na C, kuma zata buga kwallo da ‘kasar Ghana, Algeria da Afirka ta Kudu, a wasannin da zasuyi wanda zai zamanto kowaye yaci wasa to zai ‘kara gaba, inkuma aka baka kashi to zaka tattara naka ya naka ka koma gida.

XS
SM
MD
LG