Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alamu Za'a Raba Gari Tsakanin Majalisar Wakilai Da Ta Dattawa A Nigeriya


Mjalisar Dattawan Najeriya

Akwai Alamun Raba Gari tsakain Majalisar Wakilan Nigeriya da ta Dattawa akan takun sakar dake tsakanin Majalisar Dattawan Fadar Shugaban Nigeriya.

Tun bayan kin amincewa da Ibrahim Magu, a matsayin shugaban hukumar yaki da masu bata dukiyar kasa ta EFCC, da shugaba Buhari, ya turawa majalisar har sau Biyu, ‘yan majalisar dattawan ke shan suka daga ‘yan Najeriya.

Dan kwamitin kasafin kudi a majalisar wakilan Najeriya, Hon. Shehu Sale Rijau, ya ce bashi tare da abinda ‘yan majalisar dattawan suke yi, domin shugaban kasa keda hurumin kawo wanda yaga ya dace, dan haka shi ya ce yana bayan shugaba Buhari, domin ya tabbatar da yana yunkurin aiwatar da gaskiya ne.

Bisa dukkan alamu majalisar wakilai na shirin takawa majalisar dattijan burki biyo bayan kin tantance kwamishinonin hukumar zabe da shugaba Buhari ya turawa majalisar dattawan kamar yadda Shehu Sale Rijau, ya yi karin bayani.

Shugaban kwamitin labarai a majalisar dattawan Hon. Aliyu Sabe Abdullahi, ya ce surutan da ake yi akan su harma da zanga zangar nuna adawa da su duk ba wani bakon abu bane a siyasa, domin duk abinda za a yi sai wani ya ce bai yi masa ba dai-dai ba.

Mustapha Nasiru Batsari na da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG