Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Dan Gari: Tarihin Kauyen Zangon ‘Yan Kwando, Kano


A yau shirin Da Dan Gari ya lalubo tarihin kauyen Zangon ‘Yan Kwando da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kanon Najeriya. 

Mai unguwar Zangon ‘Yan Kwando Malam Bala Adamu Idris, ya ce ‘yan kasuwa da ke zuwa daga jihar Katsina da sauran wurare ne suka kafa kauyen, ma’ana asali garin fili ne na kasuwanci.

Malam Adamu ya kuma ce a shekarar 1958 aka kafa garin kuma mutanen jihar Borno ne wadanda suka fara zama wurin.

Kauyen, wanda ake wa kirari da “Zangon ‘Yan Kwando madafa tuwo garin Dan Gage,” ya shahara a sana’ar kwando wanda ake sakawa da itatuwa, kuma ana kai kwandunan zuwa sassan Najeriya daban-dabam, har ma da makwabtanta.

Game da kalubalen da suke fuskanta a kauyen, mai unguwar ya ce suna bukatar gwamnati ta taimaka wa makarantun su na firamare saboda dalibai na fama da rashin kujeru bayan haka akwai matsalar ruwan sha da suke fama da ita, duk da cewa suna da rijiyoyin burtsatse, amma wasunsu sun daina aiki.

Ga cikakken shirin cikin sauti Daga Freedom Rediyo, Kano.

Da Dan Gari: Tarihin Kauyen Zangon ‘Yan Kwando, Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:07:45 0:00


XS
SM
MD
LG