Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Dan Gari: Tarihin Masarautar Uke, Jihar Nasarawa


A yau shirin Da Dan Gari ya ziyarci masarautar Uke da ke karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa, wadda aka kafa tun a shekarar 1804, a cewar basaraken garin.

Sadiq Abbas, na gidan radiyo da talabijin na jihar Nasarawa, ya yi hira da mai Martaba Yakanaje na Uke, Alhaji Ahmed Abdullahi Hassan, wanda ya bayyana cewa masarautar ta samo asali ne a karkashin jagorancin Mujaddadi Mahamud Tuni, wanda ya jagoranci karbo tuta daga Ubare, kuma asali wadanda suka kafa masarautar daga garin Getso a karamar hukumar Gwarzo da ke jihar Kano suka fito.

To ko me sunan “Yakanaje” ke nufi, mai Martaba Ahmed ya ce wani jinsi ne na al’umar Fulani da asali aka sansu da fararen shanu.

Saurari cikakken shirin cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:10:19 0:00


Dubi ra’ayoyi

XS
SM
MD
LG