Accessibility links

Sabili da wasu dalilai na tsaro gwamnatin jihar Neja ta haramta yin achaba da kabu-kabu a jihar daga ranar 2 ga watan Janairun shekarar 2014.

A kokarin tabbatar da tsaro a jihar Neja gwamnatin jiharr ta haramta sana'ar achaba da kabu-kabu daga watan Janairun shekara mai zuwa.

Kodayake sanarwar ta gwamnati ta haramta sana'ar achaba da kabu-kabu cikin babban birnin jihar ne, wato Minna, tuni jama'a suka soma tofa albarkacin bakinsu a duk fadin jihar.

Kwamishanan sadarwa na jihar Alhaji Garba Mohammed ya ce sun zauna a jamalisar zartaswa sun tsayar da shawarar aiwatar da dokar daga biyu ga watan Janairu mai zuwa domin inganta tsaro. Duk wanda ya karya dokar daga wannan ranar za'a kamashi a kuma hukuntashi. Ya ce akwai tara da za'a ci duk wanda ya saba ma dokar.Matakin yana da alaka ne da matsalar harkokin tsaro a jihar. Kwamishanan ya ce kwanakin baya ana anfani da achaba da kabu-kabu ana kashe 'yansanda da mutane.

Domin samar ma masu sana'ar achaba da kabu-kabu aikin yi gwamnatin jihar ta ce ta yi tanadin keke napep har guda dubu daya domin maye gurbin achaba da kabu-kabu.

To sai dai su 'yan achaban sun ce keke napep dubu daya basu ishesu ba. Awaisu Mohammed mai sana'ar kabu-kabu ya ce matakin da gwamnati ta dauka abun bakin ciki ne wurinsu. Domin idan mutum yana da sana'a da yake samun biyan bukata da ita amma aka wayi gari aka ce an hana sana'ar abun bakin ciki ne. Shi ma Idris Aliyu wanda ya ce shi dan kabu-kabu ne mai karfi domin ya yi shekar goma yana sana'ar ya ce matakin a bun bakin ciki ne garesu domin basu da wata sana'ar

Shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar ya ce dokar ta takurawa mutane. Ya ce ba'a yin doka a ba mutane sati biyu kawai. Ya ce sana'ar achaba na taimakawa mutane ainun. Ya ce yadda aka ce za'a dauke gaba daya bai dace ba. Akwai wasu hanyoyi da yakamata a bi.Ya ce duk wadanda suke sana'ar achaba a nemesu a basu keke napep. Kada a ba wasu a hana wasu kamar yadda lamarin ke faruwa yanzu.

Mutapha Nasiru Batsari nada rahoto.

XS
SM
MD
LG