Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daga Ibadan Oyon Najeriya Mutane Sun Furta Albarkacin Bakinsu Akan Nasarar Trump


Donald Trump sabon shugaban Amurka mai jiran gado

A sakamakon nasarar da Donald Trump yayi a zaben shugaban kasar Amurka inda ya kada Hillary Clinton 'yan Najeriya na cigaba da tofa albarkacin bakunansu.

Wani Malam Kasumu yace shi yayi mamaki da nasarar da Donald Trump ya samu saboda shi bai yi tsammanin zai ci ba.

Yace abubuwan da mutane suke fadi sun sa ya dauki ita Hillary Clinton ce zata ci nasara amma sai gashi bata samu ba. Shi Trump da ya ci lokacinsa ne yayi. Yana kyautata zaton Trump zai kawo canji a Amurka.

Shi kuwa Garba daga Kano yace zaben bai yi masa dadi ba saboda Hillary Clinton suka fi son ta ci domin bata kyamar musulmi. Shi kuwa Trump yana kyamar musulmi har ma yace baya son su shiga kasar Amurka.

Sanusi Saidu daga Sokoto yace sakamakon zaben bai zo masa da mamaki ba saboda Allah ya kan yi abunsa yadda ya ga dama amma ba dadi saboda abun da ya fada akan musulmai da bakar fata.

Shi ko Muhammad Yusuf yace zabe yayi kyau kuma sun yi murna saboda yace ba zai bar musulmai su shiga Amurka ba to suna son su g abun da zai yi idan sun shiga kasar.

Amina tace tsakaninta har ga Allah bata ji dadin kayen da aka yiwa Hillary Clinton ba haka kuma mata 'yanuwanta basu ji dadi ba saboda suna so ta ci ta kwatowa mata 'yanci.

Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00

XS
SM
MD
LG