Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daga Ibadan Wasu 'Yan Najeriya Sun Bayyana Ra'ayinsu Kan Zaben Amurka


Hillary Clinton da Donald Trump

Wasu mazauna birnin Ibadan fadar gwamnatin jihar Oyon Najeriya sun bayyana ra'ayinsu akan zaben shugaban kasar Amurka musamman akan 'yan takaran dake kan gaba wato Hillary Clinton da Donald Trump

Yau za'a gudanar da zaben Amurka kuma masu fafutikan neman a zabesu sun kammala yakin neman zabe da jawabai daban daban tare da jadadda alkawuran da suka yiwa jama'a.

A birnin Ibadan wasu sun bayyana ra'ayinsu akan zaben. Alhaji Junaidu Mai Shayi yayi fatan Allah ya sa a yi zaben lafiya a kuma gama lafiya. Yace duk wanda ya ci zaben ya tuna da kasashen Afirka musamman da irin rashin zaman lafiya da ake yi a kasashen yammacin nahiyar sanadiyar rikicin 'yan ta'ada. Rikicin ya fi addabar kasar Najeriya da makwaftanta. Ya kira Amurka ta fuskanci Naigeriya da idon rahama.

Shi kuma Ado Suleiman sarkin Hausawan Akinyele yana fatan Allah ya ba Hillary Clinton saboda ita ba zata yi yaki ba. Idan kuma babu yaki Amurka zata maida hankali akan taimakon kasashen Afirka. Idan Clinton taci Najeriya zata samu damar kai halin kuncin da take ciki gaban Amurka da nufin samun taimako.

Shi ko George Bello yana son Donald Trump ya ci zaben ko watakila zai taimakawa Najeriya kan tattalin arzikinta. Yana ganin idan Trump ya hau zai taimakawa Afirka a kawar da kuncin rayuwa saboda wai yana da kudi.

Hajiya Abeti tace duk wanda ya ci zabe a Amurka a bashi.Wanda kuma yaci ya yiwa Allah ya taimakawa Buhari da kudi saboda Najeriya ta shiga wani halin. Ya taimaka da tsaro.

Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00

XS
SM
MD
LG