Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dage Zabe ba Zayyi Maganin Komai ba


Zaben a Najeriya. (File Photo)
Zaben a Najeriya. (File Photo)

An maidawa Sambo Dasuki martani akan dage zabe.

Kungiyar majalisar, Limaman masalatan Jumma’a, a jihar Neja, dake tarayyar Najeriya, ta mayar da martini akan shawarar da mi baiwa shugaban Najeriya, shawara akan harkokin tsaro, kanar Sambo Dasuki mai ritaya, ya baiwa hukumar zaben Najeriya, data dage lokacin zaben kasar.

A wani taron manema labarai, da majalisar Limaman ta kira tace sam bata tare da wannan shawara, a ranar alhamis din nan ne dai aka ruwaito cewa Sambo Dasuki, yana bada wannan shawarar a wata cibiyar bincike birnin London, ta kasar Ingila.

Sakataren majalisar Limaman, Imam Umar Faruk, yace “Dage zabe ba zayyi maganin komai ba, a halin da ake ciki yanzu, bazata sake zani ba, duk lokacin da aka kai shi idan lokacin ya matso ‘yan takarar sunanan zasu sake fitowa wanda ke kai bai so ya sauka saboda haka da yanzu da wancan lokacin duk daya ne, yanzu ne ma muka san mai muke ciki gobe mai zai faru Allah kaidai ya sani, maganin alamarin nan ayi gaskiya.”

A halin da ake ciki dai majalisar Malaman, dace ta dukufa wajen gabatar da hudubobi a Masallatai na Jumma’a, dake jihar ta Neja domin nuna mahimmancin yin zabe lafiya.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

XS
SM
MD
LG