Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Iraki Sun Fatattaki ISIS Daga Mosul


Firaminista Haider al-Abadi a Birnin Mosul rike da Tutar Iraki

Sojojin Iraki Sun Kwace birnin Mosul daga hannu kungiyar ISIS inda aka kwashe kwanaki ana barin wuta.

Kasar Iraki ta ayyana yin nasara kan kungiyar ISIS, bayan da sojojinta su ka sami nasarar kwace birnin Mosul kwata-kwata daga hannun ISIS.

"Babban Kwamandan sojojin Iraki, Firaminista Haider al-Abadi, ya iso cikin birnin Mosul wanda aka bukutar kuma ya jinjina ma gwarazan sojojin kasar da ma mutanen kasar saboda wannan babbar nasarar," a cewar wata takardar bayani da ta fito daga ofis dinsa a yau dinnan Lahadi.

To amma an cigaba da yaki har zuwa lokacin da ake ta shagulgula, ta yadda ma har ake ta jin karar harbe-harbe a birnin na Mosul da kuma hare-haren jiragen sama da ake kaiwa a sassan birnin a daidai lokacin da ofishin Firaministan ya fitar da takardar bayanin.

Sojojin Iraki sun yi amfani da hare-haren jiragen saman da sojojin gamayya ke kaiwa da kuma goyon bayan da su ke sama ta kasa, wajen kai farmakin sake kwato Mosul, wanda shi ne birni mafi girma da ISIS ta kwace a farmakin da ta kai shekaru uku da su ka gabata, lokacin da kungiyar mai tsattsauran ra'ayi ta yi shelar kafa daularta a sassan Irakin da Siriya.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG