Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Najeriya Sun Fara Sabon Farmaki Kan 'Yan Boko Haram A Borno


Sojojin Najeriya dake jihar Borno yanzu

Biyo bayan wani sabon salon da kungiyar Boko Haram ta soma anfani dashi dakarun Najeriya sun maida martani ta shirya wani sabon farmaki a karkashin jagorancin Manjo Janar Abba Diko da lakabin "Operation Last Hold."

Babban hafsan sojojin Najeriya dake kula da aiakace aikace Manjo Janar David Ahmadu ya bayyana wani sabon farmaki da zasu fara kaiwa kan 'yan Boko Haram a arewacin jihar Borno mai taken "Operation Last Hold"

Sabon farmakin ya zama wajibi ne saboda yadda aika aikar kungiyar ta'addancin ya dauki wani sabon salo. Tuni sojojin suka girke manyan kayan yaki tare da sojojin kundunbala. Manufar sabon matakin shi ne a samu a rugurguza kungiyar gaba daya a zirin yankin tafkin Chadi, kamar yadda rundunar mayakan Najeriya tayi bayani.

Wannan sabon farmakin za'a dauki watanni hudu ana yin sa domin a kakkabe 'yan kungiyar ta'addancin a yankin tafkin Chadi, kamar yadda Manjo Janar David Ahmadu ya fada.

Da yake sharhi kan wannan sabon yunkurin, Aliko El-Rashid Haroun, wani tsohon jami'in leken asirin sojoji, ya gargadi dakarun na Najeriya da su yi la'akari da makwabciyar jihar Bornon, wato arewacin jihar Yobe, musamman tsakanin Yoben da Jamhuriyar Nijar. Ya ce idan aka lura, yankin ne mutanen Mamman Nur suke.

Wannan sabon farmakin Manjo Janar Abba Dikko ne zai jagorance shi.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:12 0:00

Facebook Forum

Ramaphosa Ya Kai Ziyara Najeriya

Lokacinda Ramaphosa Ya Isa Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG