Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun 'Yan Tawaye Da Amurka Ke Marawa Baya Sun Yi Yunkurin Kwato Birnin Raqqa


Dakarun 'yan tawaye a Syria da ake kira Syrian Democratic Forces wadanda Amurka take marawa baya, yau Talata suka kaddamar da hari da zummar kwato birnin Raqqa daga hanun mayakan sakan ISIS.

Tun a cikin watan Nuwambar bara ne kungiyar ta SDF a takaice take kokarin yiwa Raqqan zobe, birni da mayakan sakai na ISIS suke dauka zaman helkwatar su.

Laftanar Janar Steve Townsend, wanda shine kwamandan runduar taron dangi da Amurka take yiwa jagoranci a fafatawa da ake yi da ISIS a Syria da Iraqi, yace yakin kwato Raqqa zai dauki lokaci kuma zai kasance da wahala, duk da haka kwato birnin zai karya lagon ISIS sosai, na ikirarinsu suna da daular Islama, kamar yadda Janar din yayi bayani cikin sanarwar da rundunar taron dangin ta fitar.

A makwabciyar Syria, watau Iraqi kuma, sojojin gwamnati dake samun goyon bayan sojojin taron dangi, suna yaki domin korar ragowar mayakan ISIS da suka rage a babbar tungar su a Mosul.

Sanarwar rundunar taron dangin tace zata ci gaba da samar da kayan yaki, da horaswa, da bayanan sirri, ga rundunar 'yan tawayen na Syria masu kokarin kwato birnin na Raqqa. Tuni 'yan tawayen suka shawarci farar hula dake birnin su fice.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG