Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Yemen Sun Kashe Akalla 'Yan Zanga Zanga 17 Jiya Litinin


Gungun masu zanga zangar nuna kin jinin gwamnati a Yemen.
Gungun masu zanga zangar nuna kin jinin gwamnati a Yemen.

Dakarun tsaron kasar Yemen sun bude wuta kan masu zanga zangar kin jinin gwamnati a birane biyu jiya Litinin, suka kashe a kalla mutane 17 suka kuma raunata wadansu da dama yayinda hukumomi suka yi watsi da yunkurin manzannin Amurka da kasashen turai

Dakarun tsaron kasar Yemen sun bude wuta kan masu zanga zangar kin jinin gwamnati a birane biyu jiya Litinin,suka kashe a kalla mutane 17 suka kuma raunata wadansu da dama yayinda hukumomi suka yi watsi da yunkurin manzannin Amurka da kasashen turai na cimma yarjejeniyar zaman lafiya.

A birnin Taiz inda dubun dubatan mutane suka shafe sama da makonni shida suna zanga zanga, ‘yan sanda kwararru harbi, da kuma wadansu mutane dauke da makamai dake cikin farin kaya, sun yi harbi kan masu zanga zangar dake kokarin kutsawa helkwatar gwamnan lardin.

Mutane da dama kuma sun jikkata a birnin da aka shiga kwana na biyu ana kazamar zanga zanga. An jiwa daruruwan mutane rauni a birnin Hudaida dake gabar bahar maliya, lokacin da jami’an tsaro suka yi amfani da barkonon tsuhuwa da kuma albarusai wajen hana masu maci zuwa fadar shugaban kasa.

A Washington ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana tashin hankalin a Yemen a matsayin “abin takaici” yayinda Amurka ke matsawa shugaban kasar Ali Abdullahi Saleh lamba ya mika mulki. Jaridar New York Times, tace ta janye goyon bayan da ta jima tana ba Mr.Saleh, ta fara tattaunawa kan sharuddan sauka daga karagar mulkinsa.

An ambaci ta bakin wadansu jami’an Amurka da na Yemen da ba a san ko su wanene ba, na cewa, matsayin Amurka ya sake fiye da mako guda da ya shige, lokacin da aka fara tattaunawar.Ma’aikatar harkokin wajen Amurka bata tabbatar da wadannan rahotannin ba.

Wani kakakin gwamnatin kasar Yemen yace jami’an diplomasiya na kasar Amurka da kuma kasashen turai suna tattaunawa da Mr. Saleh yayinda suka kuma nemi sanin ra’ayin shugabannin hamayya dangane da yadda mika mulkin zai kasance.

Da suke maida martani jiya asabar, ‘yan hamayya sun bayyana matsayinsu ga jami’ar Amurka da cewa, tilas ne Mr. Saleh ya sauka daga karagar mulki ba tare da bata lokaci ba, ya kuma mika mulki ga gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Abd al-Rab Mansu al-Hadi,har sai an gudanar da sabon zabe.

An kuma bukaci yiwa jami’an tsaro garambawul karkashin “majalisar soji”.

XS
SM
MD
LG