Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakatar Da Zirga Zirgar Jiragen Sama A Syria Zai Sa A Cimma Bukata


Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya fada a jiya Laraba cewa muddin ana son a ceto yarjejeniyar tsagaita wuta dake neman tabarbarewa a Syria, to sai an dakatar da zirga-zirgar jiragen saman yaki a kan wasu muhimman yankuna na kasar, ciki har da wurare da kungiyoyin agaji suke neman isar da abinci da mugunguna.

Bayan dimbin matrakan da Amurka da Rasha suka sha dauka na karya ka’idojin wannan yarjejeniyar a Syria, a farko farkon wannan wata, musamman harin baya-bayan nan na jiragen sama da aka kaiwa ayarin ayarin motocin dake dauke da kayan agaji a ranar Litini wanda Amurka ta zargi Rasha, Kerry yace dukan bangarorin biyu suna fuskantar lokaci na fadar gaskiya.

Kerry dai yayi anfani da lafazin diplomasiya inda bai ware bangare daya na Syria ko Rasha don dora musu laifin kai farmakin ba, duk da cewa sune ake zargi da laifin kai galibin duk hare haren da aka kai a yankunan fararen hula, wanda kuma ya janyo mutuwar mutane da dama.

To amma Ministan harkokin wajen Rasha Serigei Lavrov da yayi jawabi a taron kwamitin sulhun kafin Kerry, bai gaggauta mayar da martini a kan shawarar Sakataren harakokin Wajen Amurkar ba, sai dai daga bisani wata mace mai Magana da yawunsa tace shawarar Amurkan holoko ne kawai.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG