Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalibai Sun Yi Zanga-zanga a Ibadan


Daliban Jami'ar Calabar a lokacin wata zanga zanga

Daliban Kwalejin Nazarin Kimiyyar a Ibadan dake Jihar Oyo a Kudu maso yammacin Najeirya, sun yi zanga zanga sakamakon rashin wutar lantarki da ruwa na tsawon makwanni uku.

Daliban sun fita tituna suna nuna rashin jin dadinsu game da rashin wutar lantarki da ruwa a dakunan kwanansu, inda suka nufi ofishin shugabannin kwalejin don mika kokensu.

Mr. Benjamin Abinbola shugaban kungiyar dalibai kuma wanda ya jagoranci zanga-zangar, ya ce, "muna zanga-zangar lumana ne domin a mayar mana da wutar lantarki da ta dauke har na tsawon makwanni uku da suka wuce."

Wani babban jami'i a kwalejin mai suna David Baba Tofe ya yi wa daliban jawabi inda ya ce makarantar za ta dauki matakan gaggawa kan matsalolin daliban.

Sai dai daliban sun sha alwashin cewa za su ci gaba da zanga-zangar muddin hukumar kwalejin ta ci gaba da ynuna halin-ko-in-kula wajen samar masu da wutar lantarki da ruwa a dakunan kwanansu.

Domin karin bayani saurari rahoton Hassan Umaru Tambuwal:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:13 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG