Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Jami'ar Damagaram Sun Ja Daga.


NIGER: Dalibai sun yi zanga zanga

Daliban Jami'ar Damagaram da ke cikin jamhuriyar Nijar sun ce muddin ba a shawo kan matsalar da ke addabar jami'ar ba, to ba za su bari ma'aikatan jami'ar su ci gaba da aiki ba.

Jamia’ar Damagaran a Jamhuriyar Nijar na fuskantar matsalar ci gaba da tafiyar da harkokin koyarwa a cikin ta.

Wannan ne yasa ministan Ilmi na kasar Yahuza Salisu Madobi yin tattaki zuwa jamia’ar domin ganawa da hukumominta da kuma na dalibai.

Sakataren kungiyar Daliban Mamman Malam Bukar yace fatar su shine a samu maslaha da zata kawo karshen matsalolin da suke addabar jamia’ar.

Malam Bukar yace kungiyar su ce ta gayyato ministan ilmi domin ya gane wa idanun sa abinda ke faruwa da niyyar ayi gyara akai.

Yace yana fata wannan tattaunawar ta zarta na zaman shan shayi da aka saba yi a lokuttan baya, domin jami’aar ta kwashe shekaru tana fama da matsaloli iri daba-daban.

Ga Tamar Abari da karin bayani 2’53:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG