Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Nake Shan Maganin Malaria - Trump


Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaba Donald Trump na kare kansa akan tallata maganin masassarar cizon sauro da kuma yin amfani da shi a matsayin kariya daga cutar COVID-19.

“Wannan zabin kai na ne,” abin da Trump ya fada kenan, ya kuma kara da cewa maganin da aka dade ana amfani da shi shekara da shekaru, wato hydroxychloroquine, an san aikinsa.”

An sha gwada shugaban lokuta da yawa amma ba ya dauke da cutar.

Babu wata kwakkwarar hujja a kimiyyance da ta nuna cewa maganin na yin kariya daga cutar ko ya na maganin cutar da coronavirus ke janyowa, wadda ta kama akalla mutum miliyan 4.8.

Wannan duk na faruwa ne bayan da shugaban ya ce yana shan maganin domin kare kansa, lamarin da ya janyo masa suka daga bangarori daban- daban duba da cewar ba a bayyana maganin a matsayin tabbataccen wanda zai iya magance cutar ta coronavirus ba.

Facebook Forum

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Hira da Yusuf, wani dan asalin Jamhuriyar Nijar da ya shekara a Abuja yana sana’r gyaran takalmi
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
XS
SM
MD
LG