Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Netflix Zai Kashe Dala Biliyan 2.5 Kan Fina-finan Koriya ta Kudu


Wani sashe na fim din Squid Game
Wani sashe na fim din Squid Game

Fina-finan Koriya da wakokinsu suna samun karbuwa a ‘yan shekarun nan a sassan duniya, idan aka yi la’akkari da farin jinin fina-finai irinsu Parasites, Squid Game da mawaka irinsu BTS.

Dandalin kallon fina-finai ta yanar gizo, Netflix ya sanar da shirinsa na kashe dala biliyan 2.5 wajen shirya fina-finan Koriya ta Kudu.

Tun a ranar Litinin Shugaban Netflix, Ted Sarandos ya yi wannan albishir bayan wata ganawa da shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk-yeol.

Yoon na ziyarar kwanaki shida a Amurka.

“Mun yanke wannan shawara ce saboda muna da kwarin gwiwa cewa dandalin shirya fina-finan Koriya ta Kudu na da labarai masu kayatarwa.” Sarandos ya ce cikin wata sanarwa.

Yoon ya kwatanta wannan sanarwa a matsayin “babbar dama” ga masu kirkirar labarai da dandalin na Netflix.

Fina-finan Koriya da wakokinsu suna samun karbuwa a ‘yan shekarun nan idan aka yi la’akkari da fina-finai irinsu Parasites da mawaka irinsu BTS.

Fim din “Squid Game” da ke ba da labarin yadda aka hada gasa mai cike da hadari tsakanin wasu mutane da bashi ya yi wa katutu, ya zamanto fim da aka fi kallo a shekarar 2021, inda ya samu sama da mutum miliyan 1.6 da suka kalla.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG