Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fim Din Ghana ‘Borga’ Ya Lashe Lambobin Yabo 3 A Bikin Gasar Fina-Finai Ta Afirka


Borga
Borga

An karrama 'ƴan wasan kwaikwayo da yawa a bikin karrama fitattun 'yan wasan fina-finai na Afirka (AMAA) na 2022 da ya gudana a Legas ranar Lahadi.

An zabi ‘Borga’ don samun lambobin yabo 15 da suka hada da Fim mafi kyau baki daya, fim mafi kyau a harshen Afirka, Babban Darakta da kuma nadar bidiyo.

Fim din, tare da hadin gwiwar 'yan kasar Ghana da Jamus, ya lashe kyautar wasan kwaikwayo mafi kyau.

Dan wasan kwaikwayo Eugene Boateng, wanda kuma yake hada shiri da ake kira frodusa na fim, ya lashe kyautar wanda yafi kwarewa a shirya wasa, mai Jagora.

Shahararren jarumin wasan kwaikwayo Adjetey Anang ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwaikwayo a lambar yabo ta mai taimako.

A halin da ake ciki, fim din Ghana mai suna ‘Road To My Father’s Compound’ wanda aka zaba a rukuni na biyar bai sami nasara ba.

Dan kasar Ghana Eugene Boateng ya doke Aaron Adatsi a wanda aka zaba a matsayin gwarzon dan wasan kwaikwayo mai jagoranci, ya doke abokin aikinsa Aaron Adatsi.

Ita ma ‘yar wasan kwaikwayo Bless Fortune ta rasa kyautar fitacciyar Jaruma a matsayin Jagora, da Ikhlas Gafur Vora ta Tanzaniya ta lashe da ta fita a wasan "Tug of War".

XS
SM
MD
LG