Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Filato Za Ta Gurfanar Da Wasu Matasa 13 A Gaban Koliya


‘Yan Sandan Najeriya
‘Yan Sandan Najeriya

Rundunar ‘yan sandan Jihar Filato ta ce matasan da ta kama take tsare da su, tana tuhumarsu ne kan sha'anin tsaro.

PLATEAU, NIGERIA - A makon jiya ne rundunar ‘yan sandan ta Jihar Filato ta cafke wasu matasa 13 a wani kogon dutse a yankin Down Base da ke karamar hukumar Jos ta Arewa.

‘Yan Sandan Najeriya
‘Yan Sandan Najeriya

A wata sanarwa daga jami’in huldar jama’a na rundunar ‘yan sandan ta Jihar Filato, DSP Alfred Alabo, ta ce kogon dutsen da ta kama matasan wuri ne da matasa ke gudanar da ayyukan asiri, shaye-shaye da sauran ayyukan da ba su dace ba.

Matasan sun karyata zargin da ake musu inda suka ce sun je wurin ne don atisayen hawan dutse.

Madam Christiana Jankam da ke zaune a yankin na Down Base ta ce a kowane mako sai an yi garkuwa da mutane biyu zuwa uku dalilin da ya sa ake maida hankalin da irin wadannan ayyukan.

Yan sanda suna binkicen wasu matasa
Yan sanda suna binkicen wasu matasa

Malam Yusuf Abdullahi Wase ya ce dole sai al’umma sun hada kai da jami’an tsaro don samun mafita.

Rundunar ‘yan sandan dai ta ce za ta gurfanar da matasan 13 a gaban kuliya, saboda sun hau dutsen ne ba tare da sun shaida wa shugabannin al’umma na yankin ba.

Saurari rahoto cikin sauti daga Zainab Babaji:

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Filato Zata Gurfanar Da Wasu Matasa Gaban Koliya Akan Batun Tsaro.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

XS
SM
MD
LG