Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Fadan Burna Boy Da Shatta Wale


Shatta Wale, Hagu, Burna Boy, dama (Hoto: Instagram - Burna Boy)

Ga dukkan alamu, an yi hannun riga tsakanin Shatta Wale da Burna Boy sanadiyyar zargin gutsiri-tsoma da ya gitta tsakanin manyan mawakan biyu a karshen makon da ya gabata.

Fitaccen dan wakar kasar Ghana Shatta Wale, ya yi wa takwaransa na Najeriya, Burna Boy wankin babban bargo bayan da ya shiga shafinsa na Instagram ya zargi Burna da yin gulmarsa.

Yayin wani jawabi da ya yi kai-tsaye ta shafin Instagram dinsa a ranar Asabar, Shatta Wale ya nuna gazawar Burna Boy da ya kasa tunkararsa ya masa magana kan wani abu da shi Shatta Wale ya yi wa Burna wanda bai masa dadi ba.

Wannan sabon rikici na zuwa ne makonni bayan rashin jituwa da aka samu tsakanin Davido da Burna Boy a Ghana inda har rahotanni suka nuna sun ba hammata iska.

Me Ya Harzuka Shatta Wale

Rahotanni da dama sun nuna cewa a lokacin bukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara, Burna Boy ya kai ziyara Ghana hakan ya sa Shatta Wale ya yi ta kiran Burna Boy a waya don su gaisa, amma Burna Boy wanda ya fito idon duniya da wakarsa ta “Killing Em” ya ki dauka.

Wasu rahotannin sun nuna cewa har sakon tes Shatta Wale ya aikawa Burna wanda an taba zabar shi sau biyu don samun lambar yabo ta Grammy Award, amma bai kula shi ba.

Bayanai sun yi nuni da cewa, Burna Boy ya fita hanyar Shattawa Wale ne, saboda ya je yana yada shi cewa ya taimaka mai ya ba shi wurin zama a Ghana a lokacin da ‘yan sandan Najeriya ke nemansa kan wani rikici da aka ce Burna Boy na da hannu a ciki, lamarin da ya sa ya tsere daga Najeriya ya tsallaka Ghana.

Shi dai Shatta Wale ya ce ya san akwai lokacin da ‘yan jarida suke hira da shi a a baya, ya fada musu cewa ya taba ba Burna Boy wurin zama a Ghana, yana mai cewa ya fadi hakan ne amma ba da wata manufa ba.

Hakan a cewar jaridar Joy ta yanzar gizo bai yi wa Burna Boy dadi ba, abin da ya sa ya je yana fadawa mutane abin da Shatta Wale ya masa.

“Me zai hana ya dauki waya ya kirani ya fada min damuwarsa, da tuni an wuce wurin mun ci gaba da dariya.” In ji Shatta Wale.

Me Burna Boy Ya Ce?

Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto Burna Boy wanda ake wa lakabi da “African Giant” bai tankawa Shatta Wale ba.

Hakazalika, bincike ya nuna cewa yau kwana uku bai wallafa wani abu a shafinsa na Instagram ba wanda hakan ya saba yadda ya saba yi a baya.

Burna Boy Da Shatta Wale Abokan Juna Ne

Abokantakar da ke tsakanin Burna Boy da Shatta Wale ba boyayya ba ce, sun jima suna hulda da juna.

A shekarar 2017 sun yi waka tare mai suna “Hosanna” wacce ta samu karbuwa a Najeriya da Ghana da ma sauran kasashen ketare.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG