Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Hajiya Naja’atu Muhammad Na Kin Karbar Mukamin Da Aka Bata


‘Yan Takarar Shugabancin Kasa na APC na Shirin Kalubalantar Jonathan, Disamba 11, 2014.

Shahararriyar ‘yar siyasar nan Hajiya Naja’atu Muhammad, tayi karin bayani kan dalilan da yasa taki karbar mukamin da gamnatin Tarayya ta bata.

Hajiya Naja’atu Muhammad, tace bata gamsu da yadda wasu ‘yan tayi dadi suka mamaye tafiyar shugaba Muhammadu Buhari ba, kuma ba tare da sunyi wa jam’iyyar komai ba.

Ko menene dalilin da yasa bata karbi wannan mukami da gwamnatin ta bata na shugabantar hukumar gudanarwa na jami’ar Tarayya dake Dutse a jihar Jigawa? Hajiya Naja’atu tace, kamar yadda ta fada shine ba a tuntube ta ba, domin anyi kulle kullen ne ba bisa ka’ida ba.

Hajiya Naja’atu dai ta koka kan yadda mutanen da basu yi komai ba a tafiyar neman yakin zaben Buhari, yanzu sune ke kaka gida a gwamnatin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:42 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG