Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Kirkiro Shirin Tallafawa Matalauta da Shugaba Buhari Yayi


 Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Mataimaki na musamman ga mataimakin Shugaba Buhari, Alhaji Hafisu Ibrahim ya bayyana abun da ya sa gwamnatin Buhari ta kirkiro da shirin tallafawa wadanda suka fi talauci a kasar.

Tallafin da aka kirkiro zai dinga ba wadanda suke cin gajiyar shirin Nera dubu biyar kowane wata.

Yace bisa da yin la'akari da irin halin da wadanda suka fi kowa talauci a kasar ya sa shugaban kasa ya fito da shirin tallafawa domin rage masu radadin kuncin rayuwa. Yace wanda ya riga ya tsufa babu abun da zai iya yi idan ba'a taimaka masa ba.

Dangane da inda aka samo kudin tallafin Alhaji Ibrahim yace a cikin kasafin kudin shekarar da ta gabata an yi tanadin nera biliyan dari biyar na tallafin.

Tsohon mataimakin gwamnan Babban Bankin Najeriya Dr. Obadiah Mailafiya yace shirin ya zo daidai lokacin da ya dace amma akwai damuwa daya. Yace a sa ido a tabbatar wadanda ya kamata su samu kudin suka samu, kada a yadda da cin hanci ko yin cuwa-cuwa da kudin.

Amma acewar Sabo Gashuwa bada tallafin ba shi ne mafita ba. Yana ganin kamata yayi a sa kudin cikin abubuwan da zasu farfado da tattalin arziki.

Jihohin Bauchi da Neja na cikin jihohin da za'a fara dasu. Misali a jihar Bauchi an fara shirin bada kudin ga mutane 10,800.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG