Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Asalin Liberia da Ya Zo Amurka Gudun Hijira Ya Zama Magajin Garin Helena a Jihar Montana, Amurka


Sabon Magajin Garin Helena, Monta,Wilmot Collins

Wilmot Collins dan Liberia wanda ya zo kasar gudun hijira ya zama magajin garin Helena a jihar Montana, jihar da bakaken jhar gaba daya basu kai kashi biyar cikin dari ba na mutanen dake jihar

Wata nasara da wasu ke mata kallon ta yi hannun babbar riga da tsautsauran shirin shugaba Donald Trump, ta kuma nuna irin tsarin da aka gina Amurka – ta yadda kowa zai iya cimma burinsa idan har ya nuna kwazo, masu kada kuri’a a Helena, babban Birnin jihar Montana, sun zabi Wilmot Collins wanda a da tsohon dan gudun hijra ne daga Liberia, a matsayin Magajin Garinsu.

Collins shi ne Ba’amurke dan asalin Afirka na farko da ya zama Magajin Gari a tarihin jihar.

“Babu shinge ga abinda kake so ka zama, da canti 25 na shigo kasar nan a aljihu na.” In ji Collins mai shekaru 54, yayin wata hira da ya yi da Muryar Amurka.

Ba dai kowa ne zai yi farin ciki da wannan nasara ta sabon Magajin Garin ba, a wannan jiha da ke yammacin Amurka mai ra’ayin mazan jiya.

Sannan Montana, na daya daga cikin jihohin da ke da dokar da ta ba da damar mallakar bindiga a Amurka.

“Hakan ya sa ni da iyalina cikin yanayi na tsoro, saboda akwai mutanen da ba su da hankali, domin ta yiwu akwai wani da ba ya so na a wannan mukami. A nan jihar Montana kowa na dauke da bindiga.” In ji Collins.

Sai dai duk da wannan fargabar, Collins ya ce zai rungumi wannan sabon matsayin na yiwa al’uma hidima.

“Masu kada kuri’a sun riga sun bayyana ra’ayinsu, sun ce, ka ga! saboda irin tarihinka, da irin iliminka na rayuwa da kake da shi, mu kai mu ke so.” A cewar Collins.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG