Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Jam'iyar Democrat A Majalisa Ya Caccaki Kasidar Nunes


Jerrold Nadler
Jerrold Nadler

Wani fitaccen dan jam'iyar Democrat a kwamitin harkokin shari'a yace kasidar da jam'iyar Republican ta fitar da ake takaddama a kai, kan binciken zargin Rasha da katsalandan, yana cike da kurakurai masu kunyatarwa.

Dan majalisar Jerrold Nadler ya bayyana a martanin da ya mayar kan kasidar da ta mamaye harkokin siyasar Amurka wannan makon cewa, kasidar da kwamitin tattarra bayanan sirri na majalisar dokokin ya fitar abin takaici ne, kuma ya kamata 'yan jam'iyar Republian a majalisa su ji kunya.

Takardar da Nadler ya rubutawa abokan aikinsa 'yan jam'iyar Democrt mai shafi shida, da tashoshin watsa labarai na talabijin suka samu, tace kasidar da ake kira Kasidar Nunes da shugaban kwamitin tattara bayanan sirri na majalisa da Devin Nunes na jam'iyar Republican ke jagoranta, an rubutata ne da gangan da nufin badda hankalin jama'a kuma tana cike da kurakurai.

Fitar da kasidar ya kara zafafa takun saka tsakanin Trump da abokan tafiyarsa 'yan jam'iyar Republican a majalisa a daya bangaren, da kuma 'yan jam'iyar Democrat da manyan jami'an hukumar binciken manyan laifuka ta FBI a daya bangaren, kan ko an sa siyasa a binciken katsalandan da ake zargin Rasha da yi a zaben shugaban kasar Amurka.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG