Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Jarida Mai Sukar Lamirin Gwamnatin Rasha Yana Asibiti Rai A Hanun Allah


Shugaban Rasha Vladimir Putin wanda ake zargin gwamnatinsa ta sama dan jaridar guba

A Rasha, matar wani dan jarida da ake kira Vladimir Kara-Murza, kuma babban dan gwagwarmaya mai sukar lamirin fadar Kremlin, tace "guba mai yawa da aka zuba ma mijintasa" ya bar shi kwance a asibiti a Moscow, rai a hanun Allah.

Yevgenia kara-Murza, ta fada jiya Talata cewa, likitoci sun ce sun gano wani abu cikin jikin mijinta da ya haddasa dakatar da aiki na galibin abunda ke cikin jikinsa. A makon jiya ne al'amarin ya auku. Koma bayan lafiyar dan jaridar, wadda rahotanni suka ce ya auku ne sa'o'i kamin ya bar kasar kan hanyarsa ta zuwa Amurka, ya tilastawa likitoci su dauki mataki mai gauni gameda dan jarida Vladimir, wanda dan shekaru 35 ne da haifuwa.

Matarsa tace, an dauki samfirin jininsa, da gashi da duka wasu sassan jiki da za'a iya gane ko an sakawa mutum guba, an tura zuwa kasashen ketare, ciki harda wata cibiyar bincike mai zaman kanta dake Isra'ila.

A birnin Washington, Senata John McCain, wanda ya juma yana cikin jerin masu sukar shugaban Rasha Vladimiri Putin, ya bayyana takaici kan lafiyar Kara-Murza, daga nan yayi hannunka mai sanda kan yiyuwar fadar Kremlin tana da hanu a rashin lafiyar dan jaridar.

XS
SM
MD
LG