Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kunar Bakin Wake Kai Hari A Moscow


Motocin jigilar marasa lafiya da na jmai'an tsaro a tsahar jiragen sama mafi girma a Moscow.

Shugaban Rasha Dmitri Medvedev ya umurci jami’an tsaro su dauki Karin matakan tsaro a dukan tashoshin jiragen sama da na kasa,bayan da wani dan kunar bakin wake ya tsrwatsa kansa a wata tashar jiragen sama mafi girma a Moscow.

Shugaban Rasha Dmitri Medvedev ya umurci jami’an tsaro su dauki Karin matakan tsaro a dukkan tashoshin jiragen sama da na kasa,bayan da wani dan kunar bakin wake ya tsrwatsa kansa a wata tashar jiragen sama mafi girma a Moscow jiya litinin, har ya kashe mutane 35.

Mr. Medvedev ya bukaci jami’an tsaro su zabura tun sawun maharan bai bace ba.Ya kira harin ta’addanci.

Shaidu suka ce sai tayu wani mutum rike da jaka ya je inda baki suke karbar kayansu dake cike makil da mutane a tashar jiragen Domodedovo ya tada nakiyoyi. Akalla kuma wasu mutane 145 sun jikkata.

Rahotani daga kafofin yada labaran Rasha sun bada labarin wata na’urar daukan hoto a tashar jiragen ta dauki hoton fashewar, kuma hukumomi suna neman wasu mutane uku dangane da wan nan hari.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin. Amma wani rahoton da kamfanin dillancinlabaran Interfax na kasar ya bayar yace an gano kan dan kunar bakin waken.

Shugaban kasashen Duniya sunyi Allah wadai da harin,inda shugaban Barack Obama ya kira harin da cewa abin takaici ne, shima babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya bayyana takaicinsa kan wan nan hari.

Kungiyar kasashen larabawa tace ta’addanci ba lamari ne da za’a lamunta da shi ba,shugaban Masar Hosni Mubarak ya kira Mr Medvedev domin yi masa jaje.

XS
SM
MD
LG