Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Sanda Ya Kashe 'Yar Jarida a Afghanistan


​Jami’an kasar Afghanistan sunce wani dan sanda ya harbe wasu mata ‘yan jaridar kasashen ketare su biyu, inda ya kashe daya sannan ya ji wa dayar rauni, gabannin zaben shugaban kasa.

‘Yar jaridar wadda ta rasa ranta, ance sunanta Anja Ni-dirin-gaus mai shekaru 48, kuma ‘yar asalin jamus ce wadda takewa kamfanin dillacin labaran AP aikin daukar hotuna. Ita kuma abokiyar aikinta Kathy Gannon yanzu dai tana jinya bayan harbinta sau biyu da dan sandan yayi.

Jami’ai since an tsare dan sandan bayan aukuwar lamarin a cikin harabar ofishin ‘yan sanda dake lardin Khost a gabashin kasar.

Kamfanin AP yace ‘yan jaridar su biyu na tafiya ne da jerin gwanon ma’aikatan zabe, masu rarraba kayan aikin zabe a mazabu dake kusa da birnin Khost, a lokacin da aka kai musu harin. A lokacin da suke cikin motarsu suna jira, sai wani kwamandan ‘yan sanda ya je inda motar tasu take, yace “Allah da Girma Yake”, sannan ya bude musu wuta da bindigarshi samfurin AK-47.

A dai-dai wannan lokaci ne Ni-dirin-gus ta mutu, amma dayar Gannon na kwance yanzu haka a asibiti.

Wannan shine karo na uku na aka kai munanan hare-hare akan ‘yan jarida makonni uku da suka wuce, kuma tashe-tashen hankula na karuwa gabannin zaben gobe asabar na duk fadin kasar, da shuwagabannin larduna.

Kungiyar Taliban ta dauki alwashin kawowa
XS
SM
MD
LG