Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Wasan Ninkaya Na Amurka Michael Phelps Nada Jimlar Gwala Gwakai 21


Rana ta hudu a wasannin Olymic da ake a Rio, ‘dan wasan Ninkayar nan na Amurka Michael Phelps ya lashe wasu kyaututtukan gwal har biyu, wanda yanzu haka yana da jimlar gwalagwalai har 21 da ya samu a rayuwarsa.

Wata jarumar ‘yar wasa daga nan Amurka, Tatie Ledecky, ya samu ‘kara samun wata kyautar gold baya da ta lashe wasan Ninkaya ta tsawon mita 200. A ranar Lahadin da ta gabata ne ta lashe wata gasar Ninkaya mai nisan mita 400, har ta lashe babbar kyautar wasan ta gold.

A bangaren wasannin guje guje da tsalle tsalle kuwa, ‘yan kungiyar Amurka sun sake daukar gold a karo na biyu a wasannin Olympic.

Sai kuma wasannin Tennis, inda ‘yar wasan Ukraine Elina Svitolina ta fitar da ‘yar wasan Amurkar nan Serena Williams a karo na uku a wasan.

Facebook Forum

Lionel Messi: PSG

A karon farko, Messi ya nuna sabuwar rigar wasan kwallonsa ta PSG
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG