Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dangin Kofi Annan Sun Yi Bankwana Ma Gawarsa


Hidimar gargajiya a shirin jana'izar Kofi Annan
Hidimar gargajiya a shirin jana'izar Kofi Annan

A shirye-shiryen jana'izar tsohon Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, jiya danginsa da sauran na kusa da su, sun yi ma gawarsa karramawa irin ta gargajiya da kuma hidimar gargajiya. Yau ake shirin bisne shi a Ghana.

A rana ta biyu a shirin jana’izar tsohon Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Anan, an bai wa danginsa damar yi ma gawarsa bankwana ta karshe.

A rana ta biyun, wato jiya, ka’idojin gargajiya ne su ka mamaye hidimar shirin jana’izar tsohon Sakatare-Janar din na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya mutu da shekaru 80 a duniya bayan wata ‘yar gajeruwar jinya.

Baya ga dangin marigayi Kofi Annan din, Ministoci, ‘yan majalisar dattawa da ‘yan majalisar wakilai, da shugabannin al’umma da sauran masu fadi a ji, wadanda sun ranar da aka kawo gawarsa Ghana su ka fara yi ma ta bankwana ta bangirma, sun cigaba da zuwa su na nuna alhili da kuma yin bankwana ga gawar Annan, a hidimar da ta hada da bushe-bushe da kuma kade-kade na musamman.

Yau Alhamis za a yi wa Annan jana’iza a Ghana, kasarsa ta haihuwa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG