Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dangote Zai Kafa Kamfanin Sarafa Manyan Motoci


Aliko Dangote wnda ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka

Yarjejeniyar bude kamfanin an yita ne tsakanin kanfanin Dangote da wani kamfanin kasar China mai suna Sino Truck

Yarjejeniyar da Alhaji Aliko Dangote ya rabtawa hannu ta kunshi kudi na dalar Amurka miliyan dari daya

Kamfanin hada motocin zai hada kimanin motoci dubu goma kowace shekara abun da masana tattalin arziki ke ganin zai habaka tattalin arzikin kasar tare da samar ma dubban mutane aiki.

Dr. Dauda Muhammad Kontagora masanin tattalin arziki da kasuwanci a jami'ar Bayero yace kafa kamfanin nada mahimmanci ga tattalin arzikin kasa saboda baicin samar wa mutane ayyukan yi za'a samu saukin lalacewar manyan motocin idan har sabbi ne..

Ta fannin biyan haraji gwamnatin tarayya zata samu kudaden shiga. 'Yan Najeriya da zasu yi aiki a ma'aikatar zasu samu damar koyon fasahar kere-kere musamman kirar mota. Za'a samu musayar fasaha tsakanin 'yan kasa da 'yan China da zasu zo suyi aiki.

A nashi bangaren Alhaji Muhammadu Baba mai kamfanin motoci mai zaman kansa yace matakin abun yabawa ne matuka musamman game da nufin gwamnatin Najeriya na ganin an fara hada motci a cikin kasar.

Yarjejeniyar ta tanadi cewa kamfanin Dangote zai mallaki kashi sittin cikin dari na kamfanin.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG