Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Darajar Naira Dai na Cigaba da Faduwa


Wani dan Nijeriya na amsar kudi a wani bani.
Wani dan Nijeriya na amsar kudi a wani bani.

Darajar Naira dai na cigaba da faduwa saboda dalilan da kwararru su ka ce sun hada da faduwar farashin man fetur a duniya.

Darajar Naira ta kara yin kasa ta yadda a yanzu Dala guda ta kai Naira 206, sannan kuma Fam guda ta kai Naira 300 sannan shi kuma Euro ya kai Naira 330, al’amarin da ke janyo fargaba kan makomar farashin kaya da kuma tattalin arziki.

Da ya ke bayani ga Aliyu Mustafa, wani mai sana’ar canji a Abuja mai suna Mohammed Nura Usman y ace Naira ta fara samun kanta a tsaka mai wuya ne tun wajen watanni uku da su ka gabata. Malam Nura ya alakanta faduwar Nairar da faduwar farashin mai a kasuwannin duniya, kamar yadda ya ce ya ji kwararru na fadi. Ya ce abin na shafar sana’arsu ta canji. Ya ce ‘yan kasuwa ne su ka fi canja dala don tafiye-tafiye kasashen kasuwanci a kasashen waje.

Da Aliyu ya tambaye shi ko ya na ganin alamar faduwar dalar za ta sassauto, sai ya ce babu alamar abin zai yi sauki nan ba dadewa ba, saboda kusan kowace sa’a guda sai ta karu. Ya ce al’amarin ya haddasa tsadar kaya a kasar.

Darajar Naira Dai na Cigaba da Faduwa - 4'10"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:10 0:00
Shiga Kai Tsaye

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG