Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Darektan Kannywood Isa Alolo "Ya Shiga Daga Ciki"


Sheikh Isa Alolo da Amaryarsa Basira (Hoto: Shafin Instagram na Isa Alolo)

Sheikh Isa Alolo, Darekta a masana’antar Kannywood da ke arewacin Najeriya, ya angwance da amaryarsa Basira.

An daura auren ne a ranar Juma’a a a jihar Kaduna da ke makwabtaka da Kano.

Bikin da ya samu halartar darektoci, furodusoshi, jarumai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finan ta Kannywood.

Daga cikin manyan darekatocin da suka halarcin daurin auren akwai Aminu Saira da Furodusa Abubakar Bashir Mai Shadda sai kuma jarumai irinsu, Umar M. Shareef da Salisu S. Fulani.

Alolo wanda har ila yau ya kan fito a matsayin jarumi, ya ba da umurni a manyan fina-finai irinsu “Ki Je Kya Gani,” da “Uwar Gulma.”

A wata hirar da ya yi da jaridar Premium Times a shekarar 2018, Alolo ya ce shiga harkar Kannywood ne a matsayin mai yin kwalliya.

“Na jima ina so na shiga harkar fim tun ina yaro, kamar yadda kowanne jarumi yake fada, amma a nawa bangaren na fara ne da yin kwalliya har na kai ga inda nake a yanzu.”

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG