Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Darikar Tijjaniya Ta Kaddamar Da Shirin Taimakon Ilimi Da Kiwon Lafiya


Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Darikar Tijjaniya a Najeriya ta yunkuro domin inganta harkokin ilimi da kiwon lafiya har ma da marayu.

Darikar Tijjaniya a Najeriya ta kaddamar da wani shirin da zai taimaka mata wajen samun kudaden da zata inganta harkoin ilimi da kiwon lafiya a maimakon dogaro da gwamnatoci da kuma mika kokon bara ga dai dai kun mutane.

Shi dai wannan tsari za a rinka saida katin shigen irin wanda ake amfani dasu a wayar salula wanda da zarar mutun ya saya ya loda sai kudi ya shiga asusun darikar Tijjaniya.

A jawabinsa a wurin taron Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yabawa wannan yunkurin na taimakon kai da kai, shima tsohon kakakin majalisar wakilai na tarayya Ghali Umar Na Abba, ya ce makasudin wannan taron shine domin wayarwa da juna kai akan alfanun gudunmawa domin taimakawa juna.

Jami’in kamfanin da ya buga katin Malam Imrana Jafaru, yace faidojin katin shine na samun kudaden domin magance matsalolin asibiti da na yara wadanda basu zuwa makaranta da kuma marayu har ma da mata masu bukatar tallafi.

Ya kuma kara da cewa duk wanda yake da katin rajista zai samu ragwame a asibiti ko makarantun da za a gina domin taimakawa al’uma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG