Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

“Daukaka Kwalejojin Ilimi Azuwa Jami’o’i Ya Dace,” in ji wani bangaren ASUU


Alamar ASUU

Rigimar da akan yi kan batun daukaka wasu kwalejojin Ilimi zuwa jami'o'in koyon aikin malanta ta dau wani sabon salo, bayan da hadakar kungiyoyin malamai da ma'aikatan Jami'o'i shiyyar Jami'ar Koyon Aikin Malanta ta Kano ta yi zargin cewa ana nan ana ta kokarin yin zagon kasa ga sabbin jami'o'in, alhalin kuwa su na iya rayuwa.

Gamayyar kungiyoyin malamai da na manyan ma’aikata na sabuwar Jami’ar koyon aikin malanta ta tarayya da ke Kano sun bayyana adawar su da yunkurin Gwamnatin Najeriya na soke daukaka darajar Kwalejojin Ilimi guda hudu zuwa Jami’o’in koyon aikin malanta da tsohuwar gwamnatin ta yi gabanin karewar wa’adinta, watanni hudu da suka gabata.

Wakilinmu a Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya ce kwalejojin Ilimin da gwamnatin da ta gabata ta daukaka darajarsu zuwa jami’o’in koyon aikin malanta su ne Kwalejin Ilimi ta Kano da ta Zariya da ta Uwere da ta Ondo, wadanda tuni ma aka nada masu shugabanni, kuma har an kara inganta gine-ginensu da kuma kayan aiki. Hasali ma, wasunsu har sun yi nisa a shirin daukar dalibai.

Bayan abin da ta kira yinkurin wasu mahassada na rushe shirin tabbatar da wadannan jami’o’in, gamayyar kungiyoyin Malamai da na ma’aikata ta kira wani taron gaggawa a Kano inda ta bayyana cewa wasu ‘yan bakin ciki da ke kafar ungulu ga daukaka darajar kwalejojin ilimi zuwa na koyon aikin malanta ne su ke tsugunta ma gwamnati bayanan da bas u ne ba. Shugaban kungiyar malaman jami’a shiyyar jami’ar ta koyon aikin malanta da ke Kano, Dr Abubakar Sadik Haruna y ace babu ruwansu da masu kokarin yin karya ma gwamnatin tarayya game da batun jami’o’in koyon aikin malantan, ya kara da cewa ba gaskiya ba ne cewa gwamnati ba za ta iya daukar nauyin wadannan jami’o’in ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG