Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

David Cameron Da Sarkozy Sun Kai Ziyara Libya


A wan nan hoto ga shugaban Faransa Nicolas Sarkozy, shugaban gwamnatin wucin gadin Libya (NTC) Prime Minister Mahmoud Jibril, da PM Britaniya David Cameron suke takawa bayan sun isa wata cibiyar kiwon lafiya a Tripoli.

Alhamis shugabannin Ingila da Faransa suka kai ziyara a biranen Libya biyu da ba a juma da ‘yanta su ba.

Alhamis shugabannin Ingila da Faransa suka kai ziyara a biranen Libya biyu da ba a juma da ‘yanta su ba, a dai dai lokacin da sojojin sabuwar gwamnatin wucin gadin kasar suka yi yunurin kai farmaki kan mahaifar Gadhafi a Sirte.

Dubban ‘yan kasar Libya ne da suke sowa suka marabci PM Ingila David Cameroon da kuma takwaransa na Faransa Nicolas Sarkozy, a babban birnin kasar Tripoli da kuma Bengazi dake gabashin kasar inda daga nan ne aka fara bore kan gwamnatin Gadhafi.

Shugabannin biyu sun fada cewa yau jumma’a zasu gabatar da wani daftarin ga MDD da zai bukaci a kafa ofishin majaisar a Libya, janye takunkumi da aka azawa kadarorin kasar, da kuma kawar da dokar hana shawagin jiragen farar hula, da kuma hanin sayarwa kasar makamai.

Sun yi alkawarin zasu tallafawa sabuwar gwamnatin kasar wajen ganin ta shimfida iko a duk fadin kasar, da kuma gano duk inda tsohon shugaban kasar da wakilan gwamnatinsa na kusa da kusa suke. Haka kuma Mr. Cameroon da Mr. Sarkozy sun yi alkawarin kungiyar NATO zata ci gaba da daukan matakan soji a kasar muddin akwai bukatar haka.

A cikin wunin jiya Alhamis din ne kuma a wani mataki na ba zata sojojijn ‘yan tawayen Libya suka fasa shingen tsaro da magoya bayan Gadhafi suka kafa suka shiga birnin Sirte, mai tazarar kilomitan 450 daga birnin Tripoli.

Dubban mayakan ‘yan tawaye daga Misrata ne suka shiga tsakiyar birnin, inda suka fuskanci tirjewa mai tsanani daga magoya bayan Gadhafi.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG