Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Direbobin Kamfanin Dangote Sun Tare Hanya Tsakanin Legas da Ibadan


Alhaji Aliko Dangote

Derebobin kamfanin Dangote sun tsare hanyar Ibadan zuwa Legas domin nuna damuwarsu dangane da rashin jin dadin aiki.

Daya daga cikin derebobin mai suna Maliki Danladi ya gaya mana, cewa su yau kusan kwanaki goma suna tsare duk wata motar kamfanin da ta zo wucewa.

Yace ana cutar su ne, shiyasa suka dauki wannan mataki domin mai kamfanin Alhaji Aliko Dangote, ya sami labari, domin ya karbo masu 'yancin su a hannun wadanda ya kafa su yi masa aiki.

Ya kara da cewa ma'aikatan da ya kafa ba aiki sukeyi ba, cutar derebobi sukeyi da cewar albashin da aka rubuta akan takarda ba shine ake biyansu ba.

Derebobin Dangote Na Rajin Aiki - 2'40"

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG